U17 Chile: Nigeria ta fara da kafar dama

Hakkin mallakar hoto marcelo Hernandez Getty Image
Image caption Nigeria ce mai rike da kofin matasa 'yan kasa da shekaru 17

Tawagar matasa 'yan kasa da shekaru 17 ta Nigeria ta fara kare kambunta da kafar dama, bayan da ta doke ta Amurka da ci 2-0 a fafatawar da suka yi a ranar Asabar a Chile.

Tawagar karkashin jagorancin kociya Emmanuel Amuneke, ta ci kwallayenta biyu ne bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci ta hannun Chukwudi Agor da kuma Victor Osimhen.

Da wannan nasarar Nigeria tana mataki na daya a rukunin farko da maki uku, bayan da Chile da Croatia suka tashi kunnen doki 1-1.

Sauran wasannin da aka kara a ranar Asabar din Guinea da Ingila suma 1-1 suka yi, sai Korea ta Kudu da ta ci Brazil daya mai ban haushi.

Kasashe hudu ne ke wakiltar Afirka a gasar da suka hada da Mali da Nigeria da Guinea da kuma Afirka ta Kudu.

Ga wasannin da za a buga a ranar Lahadi:

  • Belgium vs Mali
  • Australia vs Germany
  • Honduras vs Ecuador
  • Argentina vs Mexico