Ballon d'Or: Wadanda ke takara a bana

Masu hasashe na ganin cewar Messi zai iya samun kyautar

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Masu hasashe na ganin cewar Messi zai iya samun kyautar

An fitar da jerin sunayen 'yan wasan da za su fafata domin cin kyautar zakaran 'yan wasan kwallon kafar duniya.

'Yan wasan Manchester City guda uku Sergio Aguero, Kevin De Bruyne da Yaya Toure na cikin 'yan wasa biyar da ke buga gasar Premier da ke cikin jerin 'yan wasa 23 da za su fafata wajen cin gasar ta Ballon d'Or.

Dan Chelsea Eden Hazard da takwaransa na Arsenal Alexis Sanchez, na cikin 'yan wasan da za su yi takarar zakaran dan kwallon kafa na duniya.

Dan wasan da ke rike da kambun zakaran kwallon kafa Cristiano Ronaldo na Real Madrid da takwaransa na Barcelona Lionel Messi, wanda ya lashe gasar a baya, suna cikin na gaba-gaba a jerin 'yan wasan da ke takarar cin gasar.

Dan wasan Wales da Real Madrid Gareth Bale shi ne kadai dan wasan Biritaniya da ke cikin jerin 'yan takarar.

Kocin Chelsea Jose Mourinho da takwaransa na Arsenal Arsene Wenger na cikin mutanen 10 da ke takarar kociyan duniya na bana.

Kazakila, kociyan Barcelona Luis Enrique, da na Bayern Munich Pep Guardiola suna cikin masu yin takarar.

Cikakken jadawalin 'yan wasan da ke takara

Sergio Aguero (Argentina/Manchester City), Gareth Bale (Wales/Real Madrid), Karim Benzema (France/Real Madrid), Cristiano Ronaldo (Portugal/Real Madrid), Kevin De Bruyne (Belgium/VfL Wolfsburg/Manchester City), Eden Hazard (Belgium/Chelsea), Zlatan Ibrahimovic (Sweden/Paris Saint-Germain), Andres Iniesta (Spain/FC Barcelona), Toni Kroos (Germany/Real Madrid), Robert Lewandowski (Poland/FC Bayern Munich), Javier Mascherano (Argentina/FC Barcelona), Lionel Messi (Argentina/FC Barcelona), Thomas Muller (Germany/FC Bayern Munich), Manuel Neuer (Germany/FC Bayern Munich), Neymar (Brazil/FC Barcelona), Paul Pogba (France/Juventus), Ivan Rakitic (Croatia/FC Barcelona), Arjen Robben (Netherlands/FC Bayern Munich), James Rodriguez (Colombia/Real Madrid), Alexis Sanchez (Chile/Arsenal), Luis Suarez (Uruguay/FC Barcelona), Yaya Toure (Côte d'Ivoire/Manchester City), Arturo Vidal (Chile/Juventus/FC Bayern Munich).

Cikakken jadawalin kociyan da ke takara: Massimiliano Allegri (Italy/Juventus), Carlo Ancelotti (Italy/Real Madrid), Laurent Blanc (France/Paris Saint-Germain), Unai Emery (Spain/Sevilla FC), Pep Guardiola (Spain/FC Bayern Munich), Luis Enrique (Spain/FC Barcelona), Jose Mourinho (Portugal/Chelsea), Jorge Sampaoli (Argentina/Chilean national team), Diego Simeone (Argentina/Atletico Madrid), Arsene Wenger (France/Arsenal).

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Ronaldo ne ya lashe kyautar 2014