Za a yi zaben shugaban Fifa 26 ga watan Fabrairu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fifa ta ce za ta yi zaben sabon shugabanta a ranar 26 ga watan Fabrairu

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta tabbatar da cewar za ta gudanar da babban taronta da kuma zabar sabon shugabanta a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Zaben da za a yi a ranar ne zai fitar da wanda zai maye gurbin Sepp Blatter wanda ya fara jan ragamar hukumar tun a shekarar 1998.

Kwamitin da'a na Fifa ya dakatar da Blatter da kuma Platini daga aiki kwanaki 90, saboda zargin cin hanci da rashawa, kuma sun musanta zargin da ake yi musu.

Platini wanda shi ne shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, da kuma Yarima Ali bin al Hussein na Jordan suna daga cikin masu son maye gurbin Sepp Blatter a zaben da za a yi a Fabrairun.

Ana kuma sa ran Shaikh Salman bin Ebrahim Al Khalifa na Bahrain zai tsaya takara, shi ma tsohon dan wasan Trinidad and Tobago, David Nakhid na son zama shugaban Fifa, sai kuma tsohon dan wasan Tottenham, Ramon Vega da shi ma ke duba yiwuwar yin hakan.