CSKA da Manchester United sun buga 1-1

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Man United ta koma ta biyu a kan teburi a rukuni na biyu

CSKA Moscow ta tashi wasa da Manchester United kunnen doki 1-1 a karawar da suka yi a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Laraba.

CSKA ce ta fara zura kwallo a ragar United ta hannun Seydou Doumbia a minti na 15 da fara tamaula.

United din ta farke kwallo ta hannun Anthony Martial saura minti 25 a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon United ta koma mataki na biyu a kan teburi a rukuni na biyu, bayan da Wolsburg ta ci PSV 2-0.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga:

  • Paris St G 0 - 0 Real Madrid
  • Man City 2 - 1 Sevilla
  • Malmö FF 1 - 0 Shakt Donsk
  • VfL Wolfsburg 2 - 0 PSV
  • Atl Madrid 4 - 0 FC Astana
  • Galatasaray 2 - 1 Benfica
  • Juventus 0 - 0 Borussia Mönchengladb