Fifa na binciken Amos Adamu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fifa na fama da takaddamar cin hanci da rashawa da ake binciken manyan Jami'anta

Kwamitin da'a na hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ya ce yana bincikar Amos Adamu dan Nigeria.

Kwamitin bai yi karin bayani kan binciken da yake yi kan Amos din ba, illa dai ya ce Adamun ya karya dokar da'ar ma'aikata ta hukumar.

A shekarar 2010 aka dakatar da Adamu tsohon mamba na kwamitin amintattun Fifa daga shiga harkokin wasannin kwallon kafa tsawon shekaru uku.

An kuma dakatar da shi ne saboda zargin ya karbi cin hanci domin mara baya da bayar da kuri'arsa kan karabar bakuncin kofin duniya.

A watan Oktoban 2013 ne dakatarwar da aka yi wa Adamu ta kawo karshe.

Adamu ya yi aiki da hukumar wasanni ta Nigeria tsawon shekaru 20, kuma an yi hasashen cewa shi ne wanda zai iya maye gurbin shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka, Issa Hayatou.