Ba zan sauya yadda nake wasa ba — Costa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Costa ya ce dole mutane su yi hakuri da shi.

Dan wasan Chelsea Diego Costa ya ce shi ba waliyyi ba ne don haka ba zai sauya yadda yake taka leda ba.

Sau biyu ana haramtawa dan wasan buga wasanni uku bayan ya taka dan wasan Liverpool Emre Can da kuma taho-mu-gamar da suka yi da dan wasan Arsenal, Laurent Koscielny.

Costa ya shaida wa Football Focus cewa,"Na kawo inda nake ne saboda salon da nake amfani da shi wajen take leda. Ba zan canza salon ba saboda kawai mutane suna maganganu."

Ya kara da cewa, "Ina tsammani kwallon kafa na da fuskar nishadantarwa da kuma fuskar yi wa mutane baro-baro. Kuma 'yan wasa suna nuna fuskonin biyu ne, don haka ya kamata mutane su saba da hakan."