Sunderland ta ci Newcastle United 3-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sunderland da Newcastle United kowannensu yana da maki 6

Sunderland ta doke Newcastle da ci 3-0 a gasar Premier wasan mako na 10 da suka kara a ranar Lahadi a filin wasa na Stadium of Light.

Sunderland ta ci kwallon farko ta hannun Adam Johnson daga bugun fenariti, aka kuma sallami Coloccini na Newcastle daga wasan saboda ketar da ya yi wa Steven Fletcher.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Billy Jones ya kara cin Newcastle kwallo ta biyu, sannan Fletcher ya kara ta uku daf da za a tashi daga wasan.

Wannan shi ne karo na shida da Sunderland ta ci Newcastle a jere a wasannin hamayya da suka kara a baya.

Da kuma wannan nasara Sunderland ta koma mataki na 18 a kan teburin Premier, yayin da Newcastle ke da maki 6 a matsayi na 19 a kan teburin.