Damben ranar Lahadi da safe ya ci 'yan kallo

Image caption Takawa tsakanin Shagon Bata daga Arewa da Nigan Kudawa babu kisa a wasan

Dambatawar da aka yi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja, Nigeria ranar Lahadi da safe ya ci 'yan kallo, domin wasanni takwas aka yi babu dan damben da ya je kasa.

Tun farko an fara wasa ne tsakanin Shagon Bahagon Babangida daga Kudu da Shagon Buzu daga Arewa, sai karawa tsakanin Shagon Mahaukaci Teacher daga Arewa da Garkuwan Shagon Mada daga Kudu babu kisa.

Karawa da aka yi tsakanin Shagon Bahagon Gurgu daga Kudu da Shagon Alhazai da kuma wasan Alin Tarara daga Arewa da Garkuwan Mai Caji shi ma babu kisa.

Damben Shagon Bata daga Arewa da Nigan Kudawa ya kayatar sai dai babu kisa, haka ma fafatawa tsakanin Matawallen Kwarkwada daga Kudu da Shagon Zamfarawa daga Arewa babu wanda ya yi nasara.

Daga karshe ne aka yi gumurzu tsakanin Shagon Sanin Kawo daga Arewa da Autan Faya daga Kudu kuma turmi biyu suka yi aka raba damben aka kuma tashi daga wasan.