An ci tarar Arsenal kan cinikin Chambers

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Arsenal tana mataki na biyu a kan teburin Premier

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ci tarar Arsenal kudi £60,000, bayan da aka same ta da laifin karya ka'ida kan cinikin mai tsaron bayanta Calum Chambers.

Hukumar ta kuma gargadi Arsenal da ka da ta kara aikata irin laifin da ta yi, ta kuma ce abin takaici ne da aka yi cinikin dan wasan tare da jami'in da bai cancanta ba kuma mara lasisi.

Arsenal ta ce ta yi cinikin ne da kyakkyawar niyya, kuma FA ta fahimci hakan.

Chambers mai tsaron baya ya koma Arsenal ne daga Southampton kan kudi £16m a watan Yulin 2014.

Haka kuma hukumar ta ci tarar wakilin Fifa, Alan Middleton kudi £30,000 da kuma dakatar da shi watanni uku, saboda rawar da ya taka a kan cinikin dan wasan.