An tuhumi Mourinho da halin rashin da'a

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chelsea tana mataki na 15 a kan teburin Premier da maki 11

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi Jose Mourinho da nuna rashin da'a kan munanan kalamai da halayya da ya nuna a karawar da West Ham ta ci Chelsea 2-1.

A ranar Asabar ce West Ham ta doke Chelsea da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 10 da suka yi a filin wasa na Boleyn Ground.

Haka kuma an sallami Mourinho da mataimakinsa Silvino Louro da kuma dan wasansa Nemanja Matic daga cikin wasan a karawar.

Hukumar ta kuma tuhumi kungiyoyin biyu da kasa tsawatarwa da 'yan wasansu, ta kuma ba su daga nan zuwa 29 ga watan Oktoba domin su kare kansu.

Chelsea na fuskantar biyan tara ta kudi £25,000 saboda 'yan wasanta biyar da aka bai wa katin gargadi a karawa biyar da aka doke ta.