Infantino ya shiga takarar kujerar Fifa

Image caption A cikin watan Fabrairu ne za a yi zaben wanda zai jagoranci Fifa

Sakatare janar na hukumar kwallon kafa ta Turai, Gianni Infantino ya shiga sahun 'yan takarar kujerar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa.

Infantino ya bi sahun Michel Platini wanda aka dakatar daga shiga harkokin tamaula tsawon kwanaki 90, domin maye gurbin Sepp Blatter.

Platini ya nanata cewar zai tsaya takarar kujerar Fifa duk da martanin da Fifa ta yi masa cewar ba za ta amince da kuri'arsa ba idan bai gama wa'adin dakatarwar da aka yi masa ba.

A cikin watan Fabarairu ne hukumar kwallon kafa ta duniya za ta gudanar da zaben wanda zai jagoranci hukumar.

Kawo yanzu Tokyo Sexwale dan kasar Afirka ta Kudu da Yarima Ali Bin Al-Hussein da David Nakhid da tsohon sakatare janar na Fifa, Jerome Champagne da shugaban kwallon kafar Liberia Musa Bility ne suke takara.