Ya kamata Liverpool ta dunga natsuwa

Image caption Liverpool tana mataki na tara a kan teburin Premier

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, ya ce ya kamata kungiyar ta kau da tsoron taka leda a duk lokacin da wasa ya juya musu baya, wanda hakan yana kawo mata koma baya.

Liverpool ta tashi wasa kunnen doki a karawar da ta yi da Southampton a gasar Premier wasan mako na 10 da suka yi a Anfield ranar Lahadi.

Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun Christian Benteke, kafin daga baya Southampton ta farke kwallon ta hannun Sadio Mane.

Klopp mai shekaru 48 ya ce 'Ya kamata mu dinga kwantar da hankali idan muna taka leda, an riga an ci mu, ba kuma karshen rayuwa ba kenan'.

Ya kuma kara da cewar 'Ban san irin wannan dari-dari a wasa ba, amma 'yan wasa suna jin matsi a jikinsu, nasan dai ba ni kadai ba ne a cikin mutanen da nasan cewar ba shi ne karshen tamaula ba'.

Kocin wanda ya maye gurbin Brendan Rodgers a farkon watannan ya ce yana ganin cin gaban da Liverpool ke yi tun komawarsa Anfield.