Newcastle ta shigar da kara kan jan katin Coloccini

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Newcastle ta hada maki 6 daga wasanni 10 da ta yi a gasar Premier

Newcastle United ta daukaka kara kan jan katin da aka bai wa Fabricio Coloccini a wasan Premier da Sunderland ta doke su da ci 3-0 a ranar Lahadi.

An kori Coloccini daga fili kafin a tafi hutun rabin lokaci, saboda hana Steven Fletcher cin kwallo da ya yi wanda ya sa aka bashi jan kati a fafatawar.

A ranar Laraba ce hukumar kwallon kafa ta Ingila za ta fara sauraren karar da Newcastle United din ta shigar.

Idan kuma har ba a cire hukuncin da aka yanke tun farko ba, dan kwallon ba zai buga wasan Premier da Newcastle za ta yi da Stoke City a gida ba a ranar Asabar.

Doke Newcastle da Sunderland ta yi ya sa ta koma mataki na 19 a kan teburin Premier.