U-17: Nigeria za ta kece raini da Australia

Hakkin mallakar hoto
Image caption A ranar Laraba ce za a buga wasannin zagaye na biyu

Tawagar matasa 'yan kasa da shekara 17 ta Nigeria za ta kara da ta Australia a wasan zagaye na biyu na cin kofin matasa 'yan kasa da shekaru 17 na kwallon kafa na duniya a ranar Laraba.

Nigeria ta kai wasan mataki na biyu ne bayan da ta ci Amurka da mai masaukin baki Chile, sannan ta yi rashin nasara a hannun Croatia a rukunin farko.

Australia kuwa ta yi rashin nasara a hannun Jamus, sannan ta yi canjaras da Mexico ta kuma doke Argentina a rukuni na uku.

Sauran wasannin zagaye na biyu na gasar da za a yi sun hada da karawa tsakanin Mexico da mai masaukin baki Chile.

Ita kuwa Brazil za ta yi gumurzu da New Zealand, sai kuma Korea ta Kudu ta kece raini da Belgium.