Za a binciki yadda FA ta dauki batun Carneiro

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na 15 a kan teburin Premier

Za a bukaci manyan jami'an hukumar kwallon kafar Ingila da su yi bayani kan yadda suka dauki batun nuna ban-banci da likitar Chelsea Eva Carneiro ta ce an yi mata.

Mambobin hadakar hukumar dake ba ta sharawa ne suka ce sun damu da yadda FA ta yi wasa-rai-rai da batun Carneiro kan zargin da ta yi.

A watan jiya ne Carneiro ta bar Chelsea bayan da Mourinho ya soke ta da rashin iya aiki.

Mourinho ya soki Dr Eva Carneiro da Jon Fearn bisa kai dauki da suka yi wa Eden Hazard a wasan da suka buga 2-2 da Swansea a gasar Premier.

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ce wannan matsalar cikin gida ce, saboda haka su kadai ne za su warware ta.