An soke jan katin da aka bai wa Coloccini

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Newcastle United tana mataki na 19 a kan teburin Premier

Newcastle United ta yi nasarar daukaka kara kan jan katin da aka bai wa Fabricio Coloccini a wasan da Sunderland ta doke ta 3-0 a gasar Premier a ranar Lahadi.

An kori Coloccini ne daga wasan bayan da ya yi wa Steven Fletcher keta, aka kuma bayar da bugun fenariti ga Sunderland.

Da wannan hukuncin Coloccini ba zai buga wasa daya ba, kuma zai bugawa Newcastle wasan Premier da za ta yi da Stoke City a ranar Asabar.

Sai dai kuma hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhumi Newcastle da kasa tsawatar wa da 'yan wasanta kan halin da suka nuna a lokacin da aka kori Coloccini daga wasan.

Hukumar ta bai wa Newcastle United daga nan zuwa ranar Juma'a domin ta kare kanta.