Man United za ta karrama Rooney

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester tana mataki na hudu a kan teburin Premier

Manchester United za ta karrama kyaftin dinta Wayne Rooney da hada masa wasa domin taimaka wa gidauniyarsa da kudin da aka samu.

Magoya bayan United ne suka bukaci kungiyar da ta karrama dan wasan bisa gudunmawar da ya bayar a fagen cigabanta.

Za a shirya wasan sada zumunta da wata kungiyar da za a sanar a nan gaba da za su kara a ranar 3 ga watan Agusta na shekarar 2016 a Old Trafford.

Dukkan kudaden shiga da aka samu a wajen kallon wasan za a bai wa Rooney, domin ya yi amfani da su a gidauniyarsa ta taimaka wa yara gajiyayyu.

Rooney ya koma United daga Eveton kan kudi fam miliyan 27 a shekarar 2004, a inda ya ci kwallaye 236.