Gasar Firimiyar Nigerian wasannin mako na 35

Hakkin mallakar hoto glonpfl Twitter
Image caption Saura wasanni hudu a kammala gasar bana

Za a ci gaba da buga gasar cin kofin Firimiyar Nigeria wasannin mako na 35 a ranar Laraba, a inda za a yi wasanni 10 a filaye daban-daban dake kasar.

Cikin karawar da za a yin Kano Pillars za ta karbi bakuncin Enugu Rangers, ita ma Enyimba za ta sauki Kwara United a Aba, da yin gumurzu tsakanin Giwa FC da Wikki Tourists.

Nasarawa United za ta ziyarci Taraba FC, yayin da Sharks da Shootings Stars su kece raini a Fatakwal, da kuma wasan da Bayelsa United za ta karbi bakuncin Abia Warriors.

Har yanzu Enyimba ce ke mataki na daya a kan teburi da maki 62, sai Warri Wolves ta biyu da maki 59 da kuma Giwa FC a matsayi na uku da maki 57.

Ga wasannin mako na 35 da za a yi:

  • Dolphins FC vs El-Kanemi Warriors
  • Giwa FC vs Wikki Tourists
  • Ifeanyi Uba vs Heartland FC
  • Sharks FC vs Shooting Stars FC
  • Taraba FC vs Nasarawa United FC
  • Enyimba Aba vs Kwara United
  • Bayelsa United vs Abia Warriors FC
  • Lobi Stars vs Warri Wolves
  • Akwa United vs Sunshine Stars
  • Kano Pillars vs Enugu Rangers