Man City ta ci Crystal Place 5-1 a Capital Cup

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Man City za ta kara da Norwich City a gasar Premier

Manchester City ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar Capital One Cup bayan da ta ci Crystal Palace 5- 1 a karawar da suka yi a Ettihad a ranar Laraba.

Bony ne ya fara ci wa City kwallo a minti na 22 da fara wasa, sai De Bruyne ya ci ta biyu, Iheanacho ya zura ta uku, Touré ya kara ta hudu daga bugun fenariti sannan Garcia Alonso ya ci ta biyar.

Palace ta farke kwallo daya daga cikin wadanda aka zura mata ta hannun Delaney saura minti 11 a tashi daga fafatawar.

Itama Liverpool ta kai wasan zagayen gaba bayan da ta ci Bournemouth daya mai ban haushi a karawar da suka yi a Anfield.

A filin wasa na St Mary Southampton ta kai wasan daf da na kusa da karshe a Capital One Cup bayan da ta ci Aston Villa 2 - 1.