Mun zabi Rasha tun kafin a kada kuria - Blatter

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A watan Fabrairu ne za a yi zaben wanda zai gaji Blatter a Fifa

Sepp Blatter ya ce tun kafin a kada kuri'ar zaben Rasha a matsayin wacce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2018, suka amince su ba ta damar.

Blatter mai shekara 79, ya fadi hakan ne a wata kafar yada labarai ta Rasha da suka tattauna kan makomar wasannin cin kofin duniya ta shekaru masu zuwa.

Haka kuma ya ce irin wannan yarjejeniyar suka cimma da aka bai wa Qatar bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2022 a kurarren lokaci da tun farko suka so bai wa kasar Amurka.

An dakatar da Blatter da kuma Michel Platini daga shiga harkokin kwallon kafa har tsawon kwanaki 90, dukkansu sun karyata cewar ba su aikata ba dai-dai ba a Fifa.

Da aka tambaye shi ko sun yi kuskuren bai wa Rasha da Qatar bakuncin gasar cin kofin duniya, sai ya ce ko kusa domin Rasha ba ta taba karbar bakuncin wasannin ba.

Ya kuma ce ya kamata ya yi ritaya daga shugabantar Fifa bayan da aka kammala gasar cin kofin duniya a Brazil, amma ya ci gaba da zama ne saboda tsoron hukumar kwallon kafa ta Turai ce za ta mamaye Fifa.