Walcott da Chamberlain za su yi jinya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Arsene Wenger ya ce ba zai yi amfani da manyan 'yan wasan nasa a wasanni uku ba.

Theo Walcott da Oxlade-Chamberlain ba za su buga wa Arsenal wasanni uku ba, sakamakon raunin da suka ji.

'Yan wasan biyu sun ji rauni ne a lokacin da suke buga karawar da Sheffield ta fitar da Arsenal daga gasar Capital One Cup a ranar Talata.

Walcott ya gamu da taruwar jini ne a kafarsa, yayin da Chamberlain zai yi jinyar tsagewar tsoka shi ma a kafarsa.

Bayan da aka tashi daga karawar kociyan Arsenal Arsene Wenger, ya ce bai kamata ya yi amfani da manyan 'yan wasansa ba.

'Yan wasan biyu ba za su buga wa Arsenal fafatawar da za ta yi da Swansea City da Tottenham da kuma karawar da za ta yi da Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun Turai ba.