U17: Nigeria ta lallasa Australia 6-0

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Najeriya ta lallasa Australia a gasar kwallon kafa ta duniya, ta 'yan kasa da shekaru 17.

Najeriya ta samu galaba kan Australia a gasar kwallon kafa ta duniya ta 'ya kasa da shekaru 17, da ci 6-0, suna kuma tana shirin haduwa da Brazil.

Victor Osimhen ne ya fara saka kwallon a raga daga bisani kuma Kelechi Nwakali da Edidiong Michael Essien da kuma Samuel Chukwueze suka sha sauran kwallayen.

Kocin Golden Eaglets, Emmanuel Amuneke ya ce, "Victor ya ji dadin wannan wasa, amma an san kwallon kafa da aikin taron dangi ne."

Ya kara da cewa, "Muna cikin masu gwazo wurin takarar cin kofin, amma Brazil ma suna da kokari, don haka sai mun kara gwazo kar su bige mu."

Nigeria da Brazil za su murza leda lokacin zagayen gabda na kusa da karshe da za a yi a birnin Vina del Mar, a ranar 1 ga watan Nuwamba.