U-17 World Cup: Brazil za ta kara da Nigeria

Tawagar matasa 'yan kasa da shekara 17 ta Brazil za ta kara da ta Nigeria a wasan mataki na daf da kusa da na karshe a Gasar cin Kwallon Kafa ta Matasa ta Duniya.

Nigeria ta kai wannan matakin ne a gasar bayan da ta lallasa Australia da ci 6-0 a karawar da suka yi ranar Laraba.

Ita kuwa Brazil ta kai wasan zagayen gaba ne bayan da ta samu nasara a kan New Zealand da ci daya mai ban haushi.

Nigeria da Brazil za su fafata ne a Chile wadda ke karbar bakunci wasannin da karfe takwas dai-dai da agogon Nigeria da Nijer a ranar Lahadi.

Nigeria, wacce ke rike da kofin, ta kuma ta lashe shi sau hudu, yayin da Brazil ta dauka sau uku.

Za kuma a buga wasa na biyu da karfe 11 na dare dai-dai da agogon Nigeria da Nijar tsakanin Croatia da Mali.