Ramires ya sabunta kwantiraginsa a Chelsea

Image caption Dan wasan kwallon kafa Ramires

Dan wasan tsakiya na Chelsea, Ramires, ya sanya hannu a kan sabuwar kwantiragi wadda za ta ba shi damar kasancewa a Stamford Bridge har zuwa shekarar 2019.

Dan wasan, mai shekaru 28 da haihuwa, ya koma kulob din ne a shekarar 2010, sannan ya buga wasanni 241 a kulob din.

Ramires ya samu nasara a gasar wasannin Premier da ta Zakarun Turai da Europa da Gasar cin Kofin Ingila da kuma Leage Cup duk a lokacin yana tare da kulob din na Chelsea.

Ramires ya ce "A cikin shekaru biyar da suka shude na samun nasarar daukar manyan kofuna. Ina fatan kasancewa ta a kulob din da kuma kara samun nasara a duk wasannin da za mu yi nan da shekaru hudu masu zuwa".