Liverpool ta doke Chelsea 3-1 a Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool za ta kara da Rubin Kazan a gasar Europa Cup

Jurgen Klopp ya fara cin wasansa na farko a gasar Premier, bayan da ya ci Chelsea 3-1 a karawar da suka yi a Stamford Bridge ranar Asabar.

Chelsea ce ta fara cin kwallo ta hannun Ramires a minti na uku da fara wasa, kuma daf da za a tafi hutu ne Liverpool ta farke kwallon ta hannun Coutinho.

Philippe Coutinho ne dai ya kara cin Chelsea ta biyu, sannan Christian Benteke ya zura ta uku a ragar Chelsea.

Da wannan sakamakon Liverpool ta hada maki 17 daga wasanni 11 da ta yi, za kuma ta fafata da Crystal Palace a wasan mako na 12.

Chelsea kuwa tana nan da makinta 11 daga wasanni 11 da ta buga, za kuma ta ziyarci Stoke City a wasan da za ta yi na gaba.