Wikki Tourists ta ci Dolphins 2-0

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Saura wasanni biyu a kammala gasar wasannin bana

Wikki Tourist ta doke Dolphins ta garin Fatakwal da ci 2-0 a gasar Firimiyar Nigeria wasannin mako na 36 da suka fafata a ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi Warri Wolves ta lallasa Bayelsa United da ci 4-0, sai Kano Pillars da ta yi rashin nasara a hannun El-Kanemi da ci daya mai ban haushi.

Heartland kuwa 3-2 ta ci Giwa FC, yayin da Abia Warriors ta yi rashin nasara a gida a hannun Enyimba International da ci daya mai ban haushi.

An gamu da tsaiko a karawa tsakanin Sunshine Stars da Lobi Stars saura minti 13 a tashi wasa, lokacin Lobi ta ci kwallo daya.

Shi kuwa wasan Nasarawa United da Sharks suna 2-2 a minti na 60 ana murza leda aka bai wa Nasarawa United bugun fenariti, wanda hakan ya sa Sharks ba ta karasa wasan ba.