Aston Vila ta dauki sabon kociya Remi Garde

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aston Villa tana mataki na 20 a kan teburin Premier

Aston Villa ta nada Remi Garde a matsayin sabon kociyanta kan yarjejeniyar shekaru uku da rabi.

Garde mai shekaru 49, ya maye gurbin Tim Sherwood wanda ya ja ragamar kungiyar watanni takwas kacal, kuma ta kore shi a ranar da Swansea ta ci Villa 2-1 a gasar Premier a Villa Park.

Garde wanda ya bar Lyon bayan da ya horas da kungiyar shekaru uku a 2014 ya ce komawa Villa wata karramawa ce da bai taba za ta ba.

Bayan da Villa ta kori Sherwood ne ta nada kociyan karamar kungiyar mai horas da matasa 'yan kasa da shekaru 21 Kevin McDonald a matsayin rikon kwarya.

Sherwood wanda ya je Villa a watan Fabrairu ya kai Villa wasan karshe a kofin FA, sai dai kuma wasa daya ya ci daga guda 10 da ya yi a gasar Premier bana.