Caf Award: Toure yana cikin 'yan wasa 10 na farko

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar bakwai ga watan Janairun 2016 za a bayyana gwarzon bana

Dan kwallon Ivory Coast Yaya Toure yana cikin 'yan wasa 10 da hukumar kwallon kafar Afirka, Caf, ta fitar, domin zabar wanda ya fi yin fice a bana.

A ranar Litinin Caf ta fitar da sunayen 'yan wasa da za a zabi wanda ya fi yin fice a Afirka, a inda Yaya Toure wanda ya lashe kyautar sau hudu yake cikinsu.

Haka kuma dan kwallon Ghana mai wasa a Ingila, Andre Ayew da kuma dan kasar Senegal mai murza leda a Southampton, Sadio Mane suna cikin 'yan takara.

Masu horas da tamaula da daraktocin tsare-tsaren tamaula da suke mambobin hukumar kwallon kafar Afirka ne za su fitar da zakaran bana.

A ranar Alhamis bakwai ga watan Janairun 2016 ne a Abuja Nigeria ake sa ran sanar da sunan wanda zai zama gwarzon dan kwallon Afirka na shekarar 2015.

Ga jerin 'yan wasa 10 da Caf ta fitar da za a zaba:

  1. Andre Ayew (Ghana & Swansea)
  2. Aymen Abdennour (Tunisia & Valencia)
  3. Mudather Eltaib Ibrahim 'Karika' (Sudan & El Hilal)
  4. Mohamed Salah (Egypt & Roma)
  5. Pierre-Emerick Aubameyang (Gabon & Borussia Dortmund)
  6. Sadio Mane (Senegal & Southampton)
  7. Serge Aurier (Cote d'Ivoire & Paris Saint Germain)
  8. Sofiane Feghouli (Algeria & Valencia)
  9. Yacine Brahimi ( Algeria & Porto)
  10. Yaya Toure (Cote d'Ivoire & Manchester City)