Tevez ya lashe kofin Argentina da Boca Juniors

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saura wasa daya ya rage a kammala gasar kasar Argentina

Carlos Tevez ya taimaka wa Boca Juniors lashe gasar kasar Argentina, kuma kofi na hudu da ya dauka a kasashe hudu.

Tevez ya sake komawa Boca da taka leda a watan Yuni, bayan da ya dauki kofin gasar Brazil da Ingila da Italiya a kungiyoyin Corinthians da Manchester United da Manchester City da kuma Juventus.

Tevez ya fara yi wa Boca Juniors wasa tun lokacin da ya zama kwararren dan kwallo a shekarar 2001 zuwa 2004, a inda ya buga mata wasanni 75 ya kuma ci kwallaye 26.

Boca ta ci wasanni 11 daga cikin 14 da ta buga tun lokacin da Tevez mai shekaru 31 ya koma can da buga mata tamaula.

An bai wa Boca kofin gasar Argentina duk da sauran wasa daya ya rage a kammala gasar bana, bayan da ta doke Tigre da ci daya mai ban haushi a ranar Lahadi.