Eva Carneiro ta maka Mourinho a kotu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na 15 a kan teburin Premier da maki 11

Kamfanin dillacin labarai na Press Association ya ce Jose Mourinho zai fuskanci shari'a bisa karar da likitan Chelsea Eva Carneiro ta shigar.

Hakan na nufin Mourinho zai gurfana a gaban kotun ma'aikata, idan har ba su sasanta kansu ba.

An dakatar da Carneiro daga gudanar da aiki a babbar kungiyar Chelsea, bayan da Mourinho ya zarge ta da yin butulci a wasan da suka buga 2-2 da Swansea a gasar Premier.

Tuni kuma lauyan Carneiro ya shigar da karar Chelsea kan yadda suka sallameta daga aikin.

A ranar 8 ga watan Augusta ne Carneiro da Jon Fearn suka kai wa Hazard dauki lokacin da ya fadi a cikin fili, amma Mourinho ya ce ba su iya aiki ba.