Real Madrid za ta kara da PSG a kofin zakaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Real Madrid da PSG suna da maki bakwai-bakwai kowannensu a rukunin farko

Real Madrid za ta karbi bakuncin Paris Saint-Germain ta Faransa a wasa na biyu na gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Talata a Santiago Bernabeu.

Paris Saint-Germain ta tashi canjaras da Madrid a wasan farko na cikin rukuni farko na gasar da suka buga a Faransa ranar Laraba 21 ga watan Oktoba.

Bayan da kungiyoyin suka buga wasanni uku kowannensu, Real Madri da PSG suna da maki bakwai-bakwai, sai Malmo ta uku da maki uku, yayin da Shakhtar Donetsk ba ta da maki a mataki na hudu.

Sauran wasannin da za a yi, Manchester United za ta karbi bakuncin CSKA Moskva wacce suka tashi kunnen doki a karawar da suka yi a Moscow.

Sevilla kuwa wacce Manchester City ta ci 2-1 a Ettihad za ta karbi bakuncin wasa na biyu ne a filin wasa na Ramon Sanchez Pizjuan.

Juventus ta Italiya wacce ta tashi canjaras da Borussia Monchengladbach kuwa, za ta kungiyar ta Jamus ne a wasa na biyu.

Ga wasannin da za a buga a ranar Talata:

  • FC Astana - Kazakstan vs Atletico de Madrid - Spain
  • Manchester United - England vs CSKA Moskva - Russia
  • PSV Eindhoven - Netherlands vs VfL Wolfsburg - Germany
  • Sevilla FC - Spain vs Manchester City - England
  • Borussia Monchengladbach - Germany vs Juventus FC - Italy
  • Shakhtar Donetsk - Ukraine vs Malmo FF - Sweden
  • Benfica - Portugal vs Galatasaray - Turkey