Manchester United ta doke CSKA Moskva 1-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption United tana mataki na hudu a kan teburin gasar Premier

Manchester United ta doke CSKA Moskva da ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin zakarun Turai da suka fafata a Old Trafford a ranar Talata.

United ta ci kwallon ne ta hannun Wayne Rooney wanda ya ci a saura minti 11 a tashi daga karawar, kuma kwallo ta 237 da ya ci wa United tun komawarsa can da murza leda.

A karawar farko a gasar da suka yi a Moscow tashi wasa kunnen doki suka yi a ranar Laraba 21 ga watan Oktoba.

Da wannan sakamakon United ta koma mataki na daya a kan teburin rukuni na biyu da maki bakwai, sai PSV ta biyu da maki shida, ita ma Wolfsburg maki shida ne da ita sai kuma CSKA ta hudu da maki hudu.

Ga sauran sakamakon wasannin da aka buga:

  • Real Madrid 1 - 0 Paris St G
  • FC Astana 0 - 0 Atl Madrid
  • Sevilla 1 - 3 Man City
  • Shakt Donsk 4 - 0 Malmö FF
  • PSV Eindhoven 2 - 0 VfL Wolfsburg
  • Benfica 2 - 1 Galatasaray
  • B M'gladbach 1 - 1 Juventus