Gerrard zai yi ritaya daga buga tamaula a 2016

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gerrard ya buga wa Ingila wasanni 114

Tsohon dan kwallon Ingila, mai taka leda a LA Galaxy, Steven Gerrard ya ce zai yi ritaya daga buga tamaula a shekarar 2016.

Gerrard mai shekara 35 wanda ya yi wa Liverpool wasanni 710 ya kuma ci mata kwallaye 186 a shekaru 17 da ya yi, ya koma Galaxy da murza leda a watan Yunin bana.

Dan wasan ya ci kwallaye biyu a wasanni 14 da ya buga wa Galaxy, kuma a karshen mako zai je Ingila domin yin fashin bakin kan wasan kwallon kafa a gidan talabijin, kafin a fara gasar Amurka a watan Janairu mai zuwa.

A makon jiya ne Seattle Sounders ta fitar da Galaxy daga wasan cike gurbi a gasar Major League ta Amurka.