U-17 World Cup: Nigeria za ta fafata da Mexico

Nigeria ta dauki kofin matasa 'yan kasa da shekaru 17 sau hudu jumulla

Asalin hoton,

Bayanan hoto,

Nigeria ta dauki kofin matasa 'yan kasa da shekaru 17 sau hudu jumulla

Tawagar Nigeria ta matasa 'yan kasa da shekaru 17 za ta kara da ta Mexico a wasan daf da karshe a gasar kwallon kafa ta matasa ta duniya a ranar Alhamis.

Nigeria ta kai wasan daf da karshe bayan da ta ci Brazil 3-0 a ranar Lahadi, ita kuwa Mexico ta kai wasan zagayen gaba ne bayan da ta doke Ecuador 2-0 a ranar Litinin.

Nigeria wacce ke rike da kofin ta lashe shi sau hudu jumulla, a inda Mexico ta dauka sau biyu a shekarar 2005 da kuma 2011.

Daya wasan daf da karshe da za a buga a gasar shi ne tsakanin Mali da Belgium da za su yi gumurzu a filin wasa na La Portada a ranar Alhamis.

Dan wasan Nigeria, Victor Osimhen shi ne jagaba a matsayin wanda yafi cin kwallaye a gasar a inda ya ci tara, sai Johannes Eggestein na Jamus da ya zura hudu a raga a mataki na biyu.

'Yan wasa uku ne suke mataki na uku a yawan cin kwallaye a raga a gasar da suka hada da Kelechi Nwakali da Samuel Chukwueze dukkansu 'yan Nigeria da kuma Fedor Chalov na Rasha wadanda suka ci uku-uku kowannensu.