Bale ba zai buga karawa da Netherlands ba

Hakkin mallakar hoto huw evans picture agency
Image caption Real Madrid za ta kara da Sevilla a gasar La Liga a ranar Lahadi

Gareth Bale ba zai buga wa Wales wasan sada zumunta da za ta yi da Netherlands ba a ranar 13 ga watan Nuwamba, sakamakon raunin da ya ji.

Bale wanda rabon da ya yi wa Real wasanni tun ranar 13 ga watan Oktoba, zai ci gaba da yin jinya a Madrid da kuma karbar horo na musamman a can.

Dan wasan bai buga wa Madrid karawa hudu a baya ba, amma ana sa ran zai iya buga mata fafatawar da za ta yi da Sevilla a gasar cin kofin La Liga a ranar Lahadi.

Shi ma Aaron Ramsey wanda ke murza leda a Arsenal ba zai buga wa Wales wasan sada zumuntar ba.