Madrid da City sun kai wasan gaba a kofin Turai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za a buga wasanni takwas a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Laraba.

Real Madrid da Manchester City sun kai wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai ta shekarar nan.

Madrid din ta kai wasan matakin gaba ne a gasar bayan da ta ci PSG daya mai ban haushi a ranar Talata, kuma hakan ya sa ta hada maki 10 a rukunin farko a matsayi na daya.

PSG tana mataki na biyu da maki bakwai, yayin da FC Shakhtar Donetsk da Malmo ke da maki uku-uku kowannensu.

Manchester City kuwa ta kai wasan zagaye na biyu ne, bayan da ci Sevilla 3-1 a Spaniya a ranar Talata, kuma hakan ya sa tana da maki tara a rukuni na hudu, sai Juventus da maki takwas a mataki na biyu.

Sauran kungiyoyi 14 suka rage da za su nemi gurbin buga wasannin zagaye na biyu a kofin, wanda za a raba jadawalin karawar a ranar Litinin 14 ga watan Disamba a Nyon.

Za kuma su fara fafatawa a wasannin zagaye na biyu tsakanin ranakun 16/17 da kuma 23/24 Fabrairu.

Ga wasannin da za a buga a ranar Laraba 04 ga watan Nuwamba:

  • Chelsea FC - England vs FC Dynamo Kyiv - Ukraine
  • AS Roma - Italy vs Bayer Leverkusen - Germany
  • FC Barcelona - Spain vs FC Bate Borisov - Belarus
  • Bayern Munich - Germany vs Arsenal FC - England
  • Olympique Lyonnais - France vs Zenit St. Petersburg - Russia
  • Olympiacos CFP - Greece vs NK Dinamo Zagreb - Croatia
  • Maccabi Tel Aviv FC - Israel vs FC Porto - Portugal
  • KAA Gent - Belgium vs Valencia C.F - Spain