Falcons za ta kara da Guinea ko kuma Senegal

Hakkin mallakar hoto Thenff twitter
Image caption Super Falcons ta lashe kofin nahiyar Afirka sau bakwai

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria, Super Falcons za ta kara da Guinea ko kuma Senegal a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Falcons da Equatorial Guinea da Ghana da Afirka ta Kudu da kuma Cote d'Ivoire ba za su buga wasannin zagayen farko na neman tikitin shiga gasar ba.

Jadawalin da hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf ta fitar ya nuna cewa Nigeria za ta buga da kasar da ta samu nasara ne a wasan da za a yi tsakanin Guinea da Senegal.

Duk wacce ta kai wasan gaba tsakanin Guinea ko kuma Senegal za ta fafata da Falcons a tsakanin 8 zuwa 10 ga watan Afirilu, su kuma buga wasa na biyu makonni biyu tsakani.

Sauran wasannin da za a yi sun hada da Equatorial Guinea za ta kara da wacce ta samu nasara tsakanin Mali da Morocco, Cote d'Ivoire kuwa za ta kece raini ne da wacce ta kai wasan zagayen gaba tsakanin Libya ko kuma Masar.

Ghana kuma za ta jira abokiyar da za ta kara da ita ne tsakanin Burkina Faso ko kuma Tunisia, Afirka ta Kudu za ta barje gumi da duk wacce ta yi nasara tsakanin Botswana ko kuma Mauritius.

Haka kuma duk wacce ta samu nasara tsakanin Zambia ko kuma Namibia za ta kece raini ne da Zimbabwe.

Kamaru ce za ta karbi bakuncin wasannin cin kofin nahiyar Afirka ta kwallon kafa ta mata karo na 10 da za a yi a shekara mai zuwa.

Super Falcons ta lashe kofin nahiyar Afirka sau bakwai a inda ta dauka a shekarar 1998 da 2000 da 2002 da 2004 da 2006 da 2010 da kuma 2014.