"Damar Arsenal ta hayewa a gasar Zakarun Turai kalilan ce"

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Arsene Wenger ya ce dole Arsenal ta fahimci cewa damar ta ta yin nasara kalilan ce.

Kociyan kulob din Arsenal Arsene Wenger, ya ce damar da kungiyar tasa ke dashi na kai wa zagaye na gaba na gasar Zakarun Turai kalillan ce, bayan da Bayern Munich ta lallasa ta da ci 5-1.

Wannan rashin nasara da kungiyar ta samu ya sa Bayern Munich ta zarta ta da digo shida a kan taeburin gasar, inda Bayern din take kan gaba sai kuma kungiyar Olympiakos da ta zamo ta biyu.

A yanzu dai Arsenal na bukatar samun nasara a kan kungiyoyin Zagreb da Olympiakos a wasanninsu na karshe, su kuma yi fatan Olympiakos ta lallasa Bayern kafin sa kai ga ci.

Sai dai Arsene Wenger ya ce kungiyar tana da sauran damar hayewa, "amma dole mu fahimci cewa damar mu ta yin nasara kalilan ce."