Ivory Coast ce kan gaba a kwallon kafar Afrika

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar kwallon kafa ta Ivory Coast ce kan gaba a Afrika

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta fitar da jerin kasashe masu karfi a wasan kwallo, inda kasar Ivory Coast ta zamo ta daya a Afrika, kuma ta 22 a duniya.

FIFA ta kuma sanya Algeria ta biyu a Afrika kuma ta 26 a duniya, yayin da Ghana ta zama ta uku a Afrika kuma ta 30 a duniya.

Najeriya ce ta goma 12 a jerin kasashen Afrika kuma ta 59 a duniya, inda Kamaru take mataki na bakwai a Afrika kuma ta 51 a duniya.

Hukumar ta FIFA ta fitar da wadannan jerin kasashen ne a rahoton da ta fitar na watan Oktoba.

Ga kadan daga cikin jerin:

1. Ivory Coast

2. Algeria

3. Ghana

4. Cape Verde

5. Senegal

6. Tunisia

7. Cameroon

8. Congo

9. Guinea

10. DR Congo