Mourinho zai warware matsalolin Chelsea — Jorge Mendes

Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Jorge Mendes ya ce Morinho ya san me ya kamata ya yi don warware matsalolin Chelsea.

Wakilin kociyan Chelsea, ya ce Jose Mourinho zai warware matsalolin da club din ke fuskanta a yanzu haka.

Mista Mendes, wanda dan kasar Portugal ne, ya shaida wa BBC cewa Mourinho ba ya bukatar sai ya tabbatar wa da kowa hakan.

Ya ce, "Ya san me ya kamata ya yi. Mutane da dama na cewa wai ba shi da zabi sai na barin kungiyar. Ni na san zai iya warware wadannan matsaloli, kuma shi ne ya fi cancanta."

Mourinho ya samu sassaucin sukar da yake sha bayan da a ranar Laraba ya doke Dynamo Kiev da ci biyu da daya a karawar da suka yi a Stamford Bride a wasan Gasar Zakarun Turai.

Kungiyar ta Chelsea ce dai ta 15 a kan teburin Gasar Premier bayan da aka ci su a wasanni 11.