Manchester United ta ci West Brom 2-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United za ta ziyarci Watford a wasannin mako na 13

Manchester United ta doke West Brom da ci 2-0 a gasar Premier wasan mako na 12 da suka yi a Old Trafford ranar Asabar.

United ta ci kwallon farko ta hannun Jesse Lingard kuma ta farko kenan da ya ci wa United karkashin jagorancin Louis van Gaal.

West Brom ta samu damar da za ta farke kwallon da aka zura mata ta hannun Saido Berahino wanda ya shiga wasan daga baya, amma bai ci ba.

Juan Mata ne ya ci wa United ta biyu daga bugun fenariti, bayan da mai tsaron baya Gareth McAuley ya yi wa Anthony Martial keta.

Wannan shi ne karon farko da United ta samu nasara a wasa, bayan da ta buga uku a baya, kuma ta hada maki 24 jumulla daga wasanni 12 da ta yi.

Ga sakamakon wasu wasannin da aka yi a ranar Asabar:

  • Bournemouth 0 - 1 Newcastle
  • Leicester 2 - 1 Watford
  • Man Utd 2 - 0 West Brom
  • Norwich 1 - 0 Swansea
  • Sunderland 0 - 1 Southampton
  • West Ham 1 - 1 Everton