Arsenal da Tottenham sun tashi kunnen doki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana mataki na biyu a kan teburi, yayin da Tottenham ke matsayi na biyar

Arsenal da Tottenham sun buga kunnen doki 1-1 a gasar Premier wasan mako na 12 da suka kara a filin wasa na Emirates a ranar Lahadi.

Tottenham ce ta fara cin Arsenal a minti na 32 da fara tamaula ta hannun Harry Kane, kuma Arsenal ta farke kwallon ta hannun Kieran Gibbs saura minti 13 a tashi daga wasan.

Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama a matakinta na biyu a kan teburi da maki 26, yayin da Tottenham ta hada maki 21 tana kuma matsayi na biyar a kan teburin.

Ita kuwa Liverpool doke ta 2-1 Crystal Palace ta yi a Anfield, sannan fafatawa tsakanin Aston Villa da Manchester City suka tashi canjaras.