Muna goyon bayan Mourinho - Asmir Begovic

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mourinho bai taba rashin nasara a wasanni bakwai ba a kakar wasa daya, tun lokacin da yake horar da Chelsea

Mai tsaron ragar Chelsea, Asmir Begovic ya ce dukkan 'yan wasan Chelsea na goyon bayan Jose Mourinho, kuma shi ne zai dawo da tagomashin kungiyar.

Chelsea ta yi rashin nasara a hannun Stoke City da ci daya mai ban haushi kuma karawa ta uku kenan da aka ci ta wasa da hakan ya sa ta koma mataki na 16 a kan teburin Premier.

Kociyan Chelsea, Mourinho bai jagoranci kungiyar ba a karawar da suka yi a filin wasa na Britannia sakamakon dakatar da shi wasa daya da hukumar kwallon kafar Ingila da ta yi.

Begovic ya ce suna goyon bayan koci Mourinho, kuma suna wasa tukuru kamar yadda ya kamata, kuma shi ne kocin da zai dawo da martabar Chelsea a fagen tamaula.

Chelsea mai rike da kofin Premier bara ta yi rashin nasara a wasanni bakwai daga cikin karawa 12 da ta yi a gasar Premier