Barcelona ta doke Villarreal da ci 3-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ranar 21 ga watan Nuwamba Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a gasar La Liga

Barcelona ta ci Villarreal 3-0 a gasar La Liga wasan mako na 11 da suka kara a ranar Lahadi a filin wasa na Nou Camp.

Neymar ne ya ci wa Barcelona kwallaye biyu a karawar, sannan Luis Suarez ya zura ta biyu daga bugun fenatiti, bayan da aka yi wa Munir El Haddadi a da'ira ta 18.

Barcelon ta hada maki 27, yayin da Villarreal ke da maki 20 a wasannin 11 da suka fafata a gasar ta Spaniya.

Barcelona za ta kara a wasanta na gaba da Real Madrid a ranar 21 ga watan Nuwamba a filin wasa na Santiago Bernabeu.