Enyimba ta lashe kofin Firimiyar Nigeria na bana

Hakkin mallakar hoto npfl twitter
Image caption Wannan shi ne karo na bakawi da Enyimba ta dauki kofin Firimiyar Nigeria

Enyimba ta dauki kofin Firimiyar Nigeria na bana, bayan da ta tashi canjaras a karawar da ta yi da Warri Wolves a wasan mako na 37 ranar Lahadi.

Bayan da aka buga wasanni 37 Enyimba tana da maki 69 a mataki na daya, sai Warri Wolves ta biyu da maki 63, yayin da Giwa FC ke matsayi na uku da maki 63.

Wannan kuma shi ne karo na bakwai da Enyimba ta dauki kofin Firimiya, a inda ta fara lashe shi a shekarar 2001 da 2002 da 2003 da 2005 da 2007 da kuma 2010.

Kungiyoyi hudu dake karshen teburi sun hada da Akwa United da Kwara United da Taraba FC da kuma Bayelsa United wacce take mataki na 20 a kan teburin

Ga sakamakon wasannin mako na 37 da aka buga:

Kano Pillars 1-0 Akwa Utd El-Kanemi 1-0 Wikki Dolphins 2-1 Heartland Giwa FC 1-0 Shooting Stars FC Ifeanyiubah 0-2 Nasarawa Utd Sharks 1-0 Kwara Utd FC Taraba 2-1 Abia Warriors Bayelsa Utd 1-2 Sunshine Stars Lobi 2-0 Rangers Enyimba 0-0 Wolves