World Cup 2018: Afirka za ta buga wasan neman gurbi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun daga ranar Laraba ce za a fara buga wasannin neman neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a Afirka

Nahiyar Afirka za ta ci gaba da buga wasannin neman gurbi biyar da za su wakilceta a gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci a shekarar 2018.

Kasar Ivory Coast da Ghana suna neman tikitin wakiltar Afirka karo na hudu a jere, a inda za su buga wasanninsu a waje.

Kasar Kamaru ce ta wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya sau hudu a jere tun daga shekarar 1990 da 1994 da 1998 da kuma 2002.

Ivory Coast wacce ke rike da kofin nahiyar Afirka za ta ziyarci Liberia, yayin da Comoros za ta karbi bakuncin Ghana.

Ita kuwa Nigeria wacce ta je gasar kofin duniya sau biyar za ta ziyarci Swaziland, Nijar kuwa ta sauki Kamaru a ranar Juma'a.

Ga wasannin da za a buga:

Laraba

 • Mozambique v Gabon
 • Sudan v Zambia
 • Thursday
 • Burundi v DR Congo
 • Namibia v Guinea
 • Benin v Burkina Faso
 • Togo v Uganda
 • Morocco v Equatorial Guinea

Juma'a

 • Madagascar v Senegal
 • Comoros v Ghana
 • Kenya v Cape Verde
 • Libya v Rwanda
 • Angola v South Africa
 • Niger v Cameroon
 • Liberia v Ivory Coast
 • Mauritania v Tunisia
 • Swaziland v Nigeria

Asabar

 • Ethiopia v Congo Brazzaville
 • Tanzania v Algeria
 • Botswana v Mali
 • Chad v Egypt
 • Gabon v Mozambique