Cristiano Ronaldo yana zaman kadaici

Hakkin mallakar hoto BBC SPORT
Image caption Ronaldo ya ce shi ne kan gaba a fagen wanda ya fi iya taka leda a duniya

Mai shirya fim din rayuwar dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya ce dan wasan yana zaman kadaici.

James Gay-Rees ya ce dan kwallon ba shi da abokai da yawa kuma yana tare da iyalansa a ko da yaushe.

Tawagar shirya fim din rayuwar Ronaldo din ta fara bin bibiyar rayuwar dan kwallon tun shekara daya da ta wuce.

Kuma James ya ce abin da yake ba shi mamaki shi ne yadda zakaran dan wasan ke tafiyar da rayuwarsa ta haskakawar da tauraronsa ke yi a yanzu.

Ya kum kara da cewa dan kwallon yana son ya kafa tarihin da za a dinga tunawa da shi a matasyin daya daga cikin fitattun 'yan kwallon kafa da aka taba yi a duniya.