Abramovich na goyon bayan Mourinho

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jose Mourinho ya ce zai dawo da tagomashin Chelsea

Har yanzu Roman Abramovich, yana goyon bayan aikin Jose Mourinho a Chelsea, kuma kociyan ba ya fuskantar barazanar kora daga Stamford Bridge.

Chelsea ta yi rashin nasara a hannun Stoke City a gasar Premier ranar Asabar da ci daya mai ban haushi, kuma Mourinho bai jagoranci karawar ba, sakamakon dakatar da shi wasa daya da FA ta yi.

Doke Chelsea da Stoke ta yi shi ne wasa na bakwai da aka ci Chelsea daga wasannin Premier 12 da ta buga, kuma tana mataki na 16 a kan teburin Premier gasar.

Rabon da Chelsea ta yi rashin nasara a wasanni bakwai daga karawa 12 a gasar Premier tun a shekarar 1978-79 lokacin ne kuma ta fadi daga gasar.

Mourinho wanda ya tsawaita zamansa a Stamford Bridge zuwa shekaru hudu a watan Agusta, ya gode wa Abramovich bisa mara masa baya da yake yi a lokacin da Southampton ta doke su.