Michu ya raba gari da Swansea City

Hakkin mallakar hoto j
Image caption Michu ya haskaka a 2013

Michu ya raba gari da Swansea City bayan da suka amince da wata yarjejeniyar ba shi wasu kudade domin ya kama gabansa.

Dan kwallon Spain din mai shekaru 29, shi ne ya fi kowanne dan kwallo zura kwallaye a gasar Premier a kakar wasa ta 2012 zuwa 2013.

A shekara ta 2012 ne, ya koma Swansea a kan fan miliyan biyu daga Rayo Vallecano.

Tun daga watan Afrilun 2014, rabon da Michu ya murza leda kuma a kakar wasan da ta wuce ya je aro a kungiyar Napoli.