Mohamed Salah zai yi jinyar rauni

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masar za ta yi kewar Salah

Dan kwallon Masar da Roma, Mohamed Salah zai yi jinya makonni hudu zuwa shida bayan da ya ji rauni a idon sawunsa.

Hakan na nufin cewa dan wasan mai shekaru 23, ba zai buga wa Masar wasannin neman cancantar bugar gasar cin kofin duniya ba tsakaninsu da Chadi.

Salah ya ji rauni a wasan da Roma ta doke Lazio a ranar Lahadi da ci biyu da nema.

Salah na haskakawa sosai a Roma a kakar wasa ta bana, watanni biyu bayan da ya bar Chelsea a matsayin aro.